<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ceto Gun Yesu LW392</title>
<lyrics>[V1]
 1) Lokacin da na faɗa cikin jaraba
 A cikin hannun magabci Shaiɗan
 Ni kan daga hannuwana a sama
 Inda cetona zai fito.

[V2]
 KORUS
 Ceto gun Yesu, jinƙai ga Allahnmu
 Nassara, salama, suna cikin hanyar Yesu

[V3]
 2)Don mine ne kake tagumi ya raina
 Don mine ne kake alhini a cikina
 Ka kafa bege ga Allahna
 Inda cetona zai fito.
 Korus

[V4]
 3) Lokacin da na yi kuka ga Allahna
 Lokacin da na yi ƙara ga kunnensa
 Lokacin da na kawo damuwata
 Allah ya ji ya ceci ni.
 Korus

[V5]
 4) Albarka ta tabbata ga Ubangiji
 Zan yabe shi dare da rana
 Mutane ku zo mu tarbi Ubangiji
 Inda cetonmu zai fito.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>392</hymn_number>
</song>